Rundunar ta ce ta kama masu laifin ne bayan wani samame da ta kai a wurarw daban-daban a jihar.
Alfijir labarai ta rawaito rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutum 26 da ake zargi da aikata kwacen wayoyi da kuma shan muggan kwayoyi.
Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a birnin Dutse.
Ya ce kamen ya biyo bayan wasu jerin samame da suka kai a tsakanin ranar 18 zuwa 19 ga watan Disamba, a kananan hukumomi hudu na jihar.
Shiisu ya ce jami’an rundunar sun kama wani matashi kan zargin satar waya da kuma sata kudi Naira 10,000 a garin Babura da ke Karamar Hukumar Babura.
Kazalika, sun kama wasu mutum biyu kan zargin laifin satar kwamfutoci shida da babur a Hadejia.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp