Tony Elemelu ya Kalubalanci Gwamnatin Tinubu Kan ta Wallafa Sunayen Barayin Dake Sace Man Najeriya

IMG 20240811 WA0143

Daga Aminu Bala Madobi

Babban hamshakin dan kasuwa a Najeriya, Tony Elumelu, ya kalubalanci gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jami’an tsaro da su gaya wa ‘yan Nijeriya mutanen da ke da hannu wajen satar danyen man fetur na kasar nan, musamman wadanda ake kwashewa a kan ruwa ta hanyar jiragen ruwa.

Alfijir labarai ta ruwaito Olumelu, Shugaban bankin United Bank for Africa (UBA) ya bayyana haka a wata hira da jaridar Financial Times ta buga a ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta, 2024.

Yawan satar mai daga bututun mai da rijiyoyi na daya daga cikin manyan kalubale musamman ga gwamnatin Tinubu, da lalata kudaden gwamnati da takaita abin da Najeriya ke fitarwa da fitar da su zuwa kasashen waje.

Najeriya, wacce ke kan gaba a tattalin arzikin Afirka, kuma babbar mai arzikin man fetur, ta yi asarar kusan ganga miliyan 620 na danyen mai – wanda darajarsa ta kai dala biliyan 46 (€42 biliyan) – tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020 kadai, a cewar wata kungiya mai fafutukar tabbatar da daidaito a masana’antu ta Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative.

Elumelu wanda yace yana fargabar kan irin satar mai ke barazana wajen karkatar da kamfanonin mai na kasa da kasa a Najeriya.

Ya ce da idonsa ya gano dalilin da ya sa kamfanonin mai na kasa da kasa ke karkatar da wasu kadarorin da ke gabar teku bayan wasu gungun masu aikata laifuka sun fara satar danyen mai a bututun sa.

Da yake magana da jaridar Financial Times, Elumelu, ya bayyana kwarin gwiwarsa, yana mai cewa, har yanzu barayin mai na kwashe kashi 18 cikin 100 na danyen mai a sashen kamfanonin sa.

Da aka tambaye shi ko wane ne ke satar mai, sai ya amsa da cewa, “Wannan satar mai ne, ba maganar satar kwalbar Coke ba ne za ka iya sakawa a aljihunka. Ya kamata gwamnati ta sani, su fada mana. Dubi Amurka – An harbi Donald Trump kuma da sauri sun san asalin wanda ya harbe shi. Ya kamata hukumomin tsaron mu su fada mana su waye ke sace mana man fetur. Kuna kai-kawo a tasoshin ruwa ruwanmu kuma ba mu sani ba?”

Dan kasuwar mai shekaru 61 ya bayyana yadda gwamnatin da ta gabata ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce ta hana shi samun rijiyar mai.

Ya bayyana cewa kamfanin Heirs Holdings ya fara neman sayan rijiyar mai tun 2017, inda ya tara dala biliyan 2.5 don kokarin siyan wata amma abinya faskara.

Sai dai a wani yanayi na daban, ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Buhari da marigayi shugaban ma’aikatan fadarsa, Abba Kyari ne suka hana yarjejeniyar.

Ya ce tabbas an gaya masa cewa Najeriya ba za ta iya barin wani abu mai mahimmanci irin wannan ya fada hannun wani kamfani mai zaman kansa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *