Tirkashi! ’Yan Sanda Sun Cafke Matasa 7 Da Makamai Tare Da Layu Kimanin 582

IMG 20231207 224557

Ya ce an kama matasan, masu shekaru 17 zuwa 21 ne a wani samame da ’yan sanda suka kai wata maboya a kasuwar garin Kalarin da Baganje

Alfijir labarai ta rawaito’Yan sanda sun kama wasu matasa bakwai kan laifin yin sojan gona da kuma layu 582, a garin Kaltungo a jihar Gombe

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce dubun waɗanda ake zargin ta cika ne inda aka kama su da makamai da tabar wiwi da tulin kwayoyi daban-daban.

Ya ce an kama matasan, masu shekaru 17 zuwa 21 ne a wani samame da ’yan sanda suka kai wata maboya a kasuwar garin Kalarin da Baganje a Karamar Hukumar Kaltungo, a ranar 3 ga watan Disamba 2023.

Ya ce abubuwan da aka samu a wajen su a matsayin kayan shaida sun hada kakin soja guda daya da hula hana-sallah, gidan harsashin bindiga kirar AK 47, da takubba da wukake da kuma gatari.

Sauran sun hada wukake da kwayar exzol, kulli 19 na tabar wiwi, kati 40 na kwayar Tramadol, layu guda 582, da kuma wata riga da aka dinka ta da layu.

Daga nan sai ya ce akwai sauran matasan da zargin, wadanda rundunar ke ci gaba da kokarin kamo su domin fuskantar shari’a.

Aminiya

IMG 20231207 WA0244 1
Alfijir Foundation

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *