Daga Baba Usman Gama
Gwamann Jihar Kano, Abba Kabir Kano, ya nada Darakta-Janar mai kula da tallace-tallace a kan titi a cikin sabbin jami’an gwamnatinsa.
Gamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu zai saya wa kansa motocin alfarma na Naira biliyan daya da miliyan daya.
NDLEA, ta ce wasu miyagu sun yi wa jami’anta kwanton ɓauna, waɗanda suke kare wani gidan ajiyar miyagun ƙwayoyi a jihar Edo.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce, idan har harin bom na farko da jirgin sojan ya kai wa masu Mauludin kuskure ne, to me ya sa bayan minti 30 suka jefa bom na biyun a kan masu aikin ceton wadanda aka jefa wa bom din farko?
Jam’iyyar PDP da NNPP da wasu jam’iyyun adawa biyar sun ƙulla ƙawancen siyasa domin fafatawa da Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Sanatan Kaduna ta Kudu, ya ce zai yi aiki tare da sauran ’yan majalisar tarayya daga jihar domin tabbatar da cewa wadanda harin bam da sojoji suka kai a yankin Tudun Biri da ke jihar adalci.
Sojoji sun harbe ’yan bindiga 3 har lahira tare da kama wasu 6 a Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Amnesty ta zargi hukumomi da ƙoƙarin rufa-rufa kan harin Kaduna.
‘Yan Arewa mazauna Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi zanga-zanga kan shari’ar zaben jihar Kano.
Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya bayyana aniyarsa ta zuwa kasar Iran, domin tattauna halin da yankin Gaza ke ciki, bayan ya ziyaraci Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Seychelles ta ayyana dokar ta-ɓaci bayan anji gagarumin fashewar wani abu.
Kotu ta kori karar jamhuriyar Nijar a kan takunkuman Ecowas.
An saki tsohon shugaban ƙasar Peru bayan shafe sama da shekaru 15 a gidan yari.
Brazil za ta tura sojojinta zuwa iyakar Venezuela.
An samar da wata kalar kwallon kafa, da za ta iya gane an tabata da hannu domin saukakawa alkalan wasa aikinsu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp