Tirka-Tirka! EFCC Sun Sake Kame Emefiele Jim Kadan Bayan DSS Suka Sake Shi

FB IMG 1646080775740

Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tatalin arzikin Nijeriya ta’annati (EFCC) ta kama tsohon gwamnan Babban Bankin ƙasa, Godwin Emefiele.

Alfijir Labarai ta rawaito EFCC ta kama Emefiele ne a jiya Alhamis da daddare, bayan sa’a guda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake shi.

Hukumar na tuhumar Emefiele kan zarge-zargen saɓa ƙa’idar aiki a lokacin da yake gwamnan CBN.

Idan mai karatu bai manta ba a watan Yuni ne dai hukumar DSS ta kama Emefiele bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *