Masarauta! An Nada Sabon Magajin Garin Zazzau

FB IMG 1698441694191 edit 59564229403409

Da yammacin yau Juma’a 27/10/2023, Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli ya tabbatar da nadin dan uwan sa (yayan shi) Alh Mu’azu Nuhu Bamalli a matsayin sabon Magajin Garin Zazzau.

Alfijir Labarai ta rawaito an nada shi ne bayan rasuwar dan uwansa, Ambasada Mansur Nuhu Bamalli makon da ya wuce.

Shi dai sabon Magajin Garin Zazzau yaya ne ga Sarkin Zazzau, kuma sati uku kenan da nada shi sarautar Baraden Zazzau, yau kuma ya zama Magajin Gari.

Shugaban ma’aikata na masarautar Zazzau, Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli (Sambo) kani ga Sarkin ya zama sabon Baraden Zazzau.

FB IMG 1698441308193
📸Zazzau

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *