Tirka-Tirka! Ɓarayi sun sace hula da sandar sarauta a fadar Sarkin Ogun

Wasu barayi sun kai farmaki fadar Olu na garin Ogunmakin da ke karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun, Oba James Sodiya, inda suka yi awon gaba da hularsa da sandar sa.

Alfijir Labarai ta rawaito an tattaro cewa a ranar Alhamis ne ɓarayin sun shiga fadar marigayi Sarkin, wanda ya rasu kimanin watanni biyu da suka gabata.

Kakakin rundunar ƴanandan jihar, Omolola Odutola, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta a yau Asabar.

Sai dai Odutola ya bayyana cewa ƴansanda sun kama mutane uku da ake zargi da aikata laifin.

Odutola, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya ce ƴansanda sun kwato hular amma har yanzu suna neman sandar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *