Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Asabar 14/10/2023 – 29/03/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya ce Olukoyede ya cika duk wasu sharuda a doka na zama shugaban hukumar EFCC.

Shugaba Tinubu ya cire birnin tarayya Abuja daga tsarin asusun ajiya na bai-ɗaya (TSA).

Gwamnan jihar Zamfara ya nanata matsayarsa ta ƙin yin sulhu da ƴan bindiga.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo mutum 3 kan zargin karkatar da akalar wata tirela da ke makare da bandir bandir na shimfidun kafet a Jihar.

Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce an magance duk wasu matsaloli, ba za a sake samun matsalar man fetur ba.

Gwamnatin Jihar Legas ta rufe kasuwar kayan gwari ta Mile 12 saboda “rashin tsafta”

An sha Biki a Kano bayan aurar da amare da angwayensu 3600 da gwamnatin jihar ta yi jiya.

An kama wani Ibrahim Abubakar, saboda amfani naira miliyan 57.7 da aka tura asusun kamfaninsa bisa kuskure a Jos, Jihar Filato.

An tsaurara tsaro a wasu biranen Amurka saboda fargaba kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa.

Rasha za ta gina tashar makamashin nukiliya a Burkina Faso.

Sojojin Isra’ila sun fara kutsawa wasu unguwannin Gaza.

Dubban Falasdinawa na ci gaba da yin gudun hijira zuwa kudancin Gaza.

West Ham na duba yuwuwar sake neman Maguire a watan Janairu idan Manchester United taci gaba da ƙin sa shi a wasanni sosai.

A shirye Manchester United take ta bar Anthony Martial ya tafi a watan Janairu.

Ajax na son ɗaukar mataimakin kociyan Manchester United Mitchell van der Gaag idan ta kori Maurice Steijn.

Sada Zumunta: Najeriya da Saudi Arabia sun tashi 2:2 a wasan jiya.

Ingila ta sami nasara akan Australia da ci 1:0 a wasan jiya.

France ta sami nasara akan Netherlands da ci 2:1 a wasan jiya.

Portugal ta sami nasara akan Slovakia da 3:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *