Tinubu Ya Sauke Shugaban Hukumar Tattara Haraji, Ya Nada Sabo


Ngelale ya ce bisa ga umarnin na Shugaban Kasa, nadin ya fara aiki nan take.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Zacch Adedeji a matsayin sabon Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS), inda ya sauke mai ci, Mohammed Nami.

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis.

Ya ce tuni Tinubu ya umarci Nami ya tafi hutun ajiye aiki na tsawon wata uku, kamar yadda dokar aikin gwamnati ta tanada a shirye-shiryen yin ritayarsa ranar 8 ga watan Disamba mai zuwa.

Ngelale ya ce bisa ga umarnin na Shugaban Kasa, nadin ya fara aiki nan take.

“Hon. Zacch Adedeji zai karbi ragamar shugabancin hukumar na tsawon kwana 90 a matsayin rikon-kwarya, kafin daga bisani a tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS), na tsawon shekaru hudu.

“Hon. Zacch Adedeji Akanta ne da ya yi karatu a Jami’ar Obafemi Awolowo, inda ya kammala da digiri mai daraja ta daya. Ba da jimawa ba ya rike muƙamin mai ba shugaban kasa shawara kan tattara haraji, bayan ya yi Kwamishinan Kudi a Jihar Oyo,” in ji sanarwar.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *