
Alfijr ta rawaito shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu amincewar majalisar dattawa domin nada sabbin mashawarta na musamman guda 20.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar shugaban kasa kan nadin mukamai na musamman guda 20 a zaman da aka yi a ranar Talata, 6 ga watan Yuni, 2023.
An samu amincewar ne bayan shugaban majalisar, Sanata Ibrahim Gobir ya mika wa majalisar bukatar ta duba bukatar shugaban kasa da kuma shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban ya bayyana shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatansa (CSO) da kuma Sen. Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan Jigawa a matsayin mataimakin COS.
Nan take aka nada tsohon ministan ayyuka na musamman George Akume. a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ