NLC Da TUC Sun Dakatar Da Shiga Yajin Aikin Da Suka Tsara.


Alfijr ta rawaito Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) tare da Kungiyar Ma’aikata  (TUC) sun dakatar da yajin aikin da suke yi shirin shiga kan batun cire tallafin man fetur.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan a daren Litinin bayan wata ganawa da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a Fadar Aso Rock.

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya da TUC da kuma NLC za su kafa kwamitin hadin gwiwa da zai duba shawarar duk wani karin albashi ko kafa tsarin da ya dace.

“Gwamnatin Tarayya da TUC da NLC za su sake duba tsarin musayar kudade na Bankin Duniya tare da ba da shawarar shigar da masu karamin karfi cikin shirin,” in ji sanarwar.

Tun da farko NLC da TUC sun yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari a ranar Laraba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *