Gwamnatin Tarayya ta ce za a jinkirta buɗe sabbin jami’o’in da gwamnatin da ta shude ta amince da kafa su.
Alfijir Labarai ta rawaito ministan Ilimi, Tahir Mamman ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba a Abuja.
Ya ce hakan ya kasance ne bisa la’akari da bukatar samar da ingantattun shirye-shirye na ilimi ga wadannan jami’o’in.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da ba da lasisi ga sabbin jami’o’in 37 daf da karshen mulkinsa.
“Da yawa daga cikin sabbin jami’o’in da gwamnatin da ta shude ta amince da kafa su ne a ƙarshen mulki.
Bayan an yi nazari da yawa, Shugaba Tinubu ya ga ya kamata a dakatar da bude su tukunna.
“Hakan ba wai na nufin za a soke jami’o’in ba ne, sai dai a duba su ta fuskar karfinsu da fa’idar da daliban za su samu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo
