Atiku Abubakar, ya bukaci Kotun Kolin Nigeria ta yi watsi da bukatar Shugaba Tinubu na kin karbar sabbin hujjojin Atikun kan zargin Tinubun da amfani da takardun bogi.
Alfijir Labarai ta rawaito Atiku ya gabatar da sabbin hujjoji ga Kotun Kolin kan zargin amfani da takardun bogi da yake cewa Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu da Tinubun ya lashe.
Ya ƙara da cewa amfani da takardun bogin da Tinubu ya yi domin rike matsayi mafi girma a Najeriya na da matukar hatsari bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya kamata a taka masa burki.
Don haka ne ya nemi Kotun Kolin da ta yi watsi da bukatar Tinubu na kin karbar sabbin hujjojin bisa hujjar sarkakiyar da za su haifar a shari’ar.
Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun (SAN) ya shaida wa kotun cewa maganar takardun shaidar karatu batu ne da ya danganci abubuwan kafin zabe, don kotun ba ta da hurumin karbar sabbin hujjoji a kansu.
A nasa bangaren lauyan Atiku, Chris Uche (SAN) ya bayyana cewa rashin karbar hujjojin ne zai haifar da karin sarkakiya, don haka ya ce karbar karin hujjojin zai tabbatar da cikakken adalci a shari’ar, “don gano gaskiyar zargin amfani da takardun bogin ko akasin haka.”
Daily Trust
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo