Tarihi! Abinda Ya Kamata Ku Sani Game Da Rayuwar Bello Galadanchi Lakabin (Dan Bello)

FB IMG 1724054528083

Daga Aminu Bala Madobi

Bello Habib Galadanchi wanda akafi sani da Dan Bello, dan asalin jihar Kano Nigeria ne, an haifeshi a kwalejin jihar Pennsylvania ta Amurka a ranar 12 ga watan Disamba, 1987, da ga Habeeb da Halisa Galadanchi. Bayan haihuwa, ya yi kuruciyarsa tare da iyalansa a Abuja babban birnin Najeriya, inda ya yi makaranta tare da ‘yan uwansa.

“Dan Bello dan asalin jihar Kano ne a arewacin Najeriya, kamar iyayensa da ‘yan uwansa.”

Duk da cewa an haife shi a Amurka, rayuwarsa da sana’arsa suna da nasaba da al’adunsa na Nijeriya, musamman al’adun Hausawa.

Kabilar Hausa, daya ce daga cikin manyan kabilun Najeriya dake kan gaba dauke da dinbin abin koyi a rayuwar kowacce al’umma, Dan Bello Musulmi ne dake bin tafarkin addinin Musulunci, imanin da ya yi tasiri a rayuwarsa, ayyukansa yakan nuna dabi’u da al’adun al’ummarsa.

Asalin al’adun Bello ya samo asali ne a Najeriya musamman jihar Kano, Inda danginsa suka fito. Ƙwararre ne cikin harshen Hausa, yana jin daɗin ƙirƙirar abubuwa cikin bankararwa da harshen sa na Hausa cikin kwarewa, yana aiwatar da aikin sa domin yayi daidaii da al’ada da dabi’un masu kyau.

Mahaifin Dan bello, wanda ke gudanar da aikin likitanci, ya kasance tare da Dan Bello, kuma ya ba shi horo na musamman a rayuwa. Ko da yake ba a san cikakken bayanai game da ’yan uwansa ba, tasirin danginsa ya bayyana karara a rayuwarsa.

“Iyayen Dan Bello da ‘yan uwansa ‘yan asalin jihar Kano ne a Najeriya.”

A tsawon zamansa da yayi a nahiyar Afrika, Bello ya yi ayyuka iri-iri, da suka hada da sayar da abinci a titi, gine-gine, da kuma taimakawa wajen gudanar da aikin likitancin mahaifinsa.

Daya daga cikin ayyukansa na farko shi ne kerawa da sayar da takalmi na hannu kamar takalmi na igiya da wasu nau’o’in takalma na musamman a Najeriya mai suna aa “kumazie.”

Bayan kammala karatun digiri a 2006, iyayensa sun ba shi ilimi a Amurka, inda Bello ya halarci Jami’ar Jihar Pennsylvania domin karantar ilimin halittun Bioengineering da Nazarin Fina-Finai da Nazarin Afirka.

Dan bello matashi ne mai hazaka, ya kammala jami’a a shekarar 2009 da digiri biyu da kananan shedun kwarewar aiki guda biyu dake nuna fasahar sa, nan take ya shiga harkar fim, inda ya shirya gajerun fina-finai irin su Charles in Arms, Unknowing Separation, Water for Baby, da kuma Taken by Storm.

Ayyukan sa na fim na farko sun samo asali ne ta hanyar gasa daban-daban da shirye-shiryen tallace tallace kuma ba da daɗewa ba ya zama sananne tsakanin jama’a.

A karshen shekarar 2011, Bello ya samu tallafi daga kungiyar fina-finan Najeriya da Nollywood, don shirya fina-finan siyasa daban-daban ga gwamnatin Najeriya.

Irin wannan dama ce ta baiwa Dan Bello, darajar sa ta karu bayan samun sabon tallafin a harkar yin fina-finai a Pennsylvania, kuma ya zama abin kallo. Agefe guda kuma, Bello ya kan shafe lokacinsa. yana aikin sa kai a cikin al’ummarsa, yana samun sabbin abokai a cikin birni da rubuta labari.

Amatsayin sa na wanda yake mazaunin kasar Amurka da Tarayyar Najeriya kuma marubuci/Darakta Bello Galadanchi, ya yi kaurin suna bayan ya samu lambobin yabo da dama a wasu gajerun fina-finai a fadin duniya. A cikin 2012, yana ɗan shekara 24 kawai, ya rubuta, ya ba da umarni kuma ya shirya fim ɗin fasalin, A Dark Place.

Kafin yin fina-finai Galadanchi ya samu digiri na farko a fannin Injiniya Biomedical. Bayan ya karanci ilimin zamantakewa, mutum ne mai taushin magana da aka saba dangantawa da aikinsa musamman cikin akasarin ayyukan da yayi a Jos, Jihar Filato ta Najeriya.

Bello shine mamallaki Gidan Hotunan Dalar, Galadanchi kuma shine wanda ya kafa kamfanin “To the Moon Productions, tare da zama jarumi R. Tariq Powell. A halin yanzu dai mai shirya fim ne yana zaune a kasar Sin inda yake koyar da yaran firamare.

Kuma a halin yanzu yana zaune tare da kyakkywar matar sa a birnin Sin, suna rayuwar su cikin farin ciki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *