Gidaje 250 Suka Ruguje Sakamakon Mamakon Ruwan Sama A Ƙauyen Natsinta Dake Jibia

FB IMG 1724055919465

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka kwashe kwanaki uku ana yi ba tare da jinkiri ba ya yi tafka ɓarna a ƙauyen Natsinta da ke ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina a Najeriya. Ruwan ya janyo rugujewar gidaje 250, lamarin da ya jefa mazauna gidajen cikin halin ƙunci da rashin tabbas.

 Alfijir labarai ta ruwaito Ɗan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Jibia, Hon. Mustafa Yusuf, wanda ya ziyarci yankin da lamarin ya shafa cikin gaggawa a ranar Asabar 17 ga watan Agusta, 2024, ya tabbatar wa mazauna yankin cewa majalisar za ta yi duk mai yiyuwa don ganin gwamnatin jihar ta samar taimakon gaggawa ga waɗanda suka rasa gidajensu.

Da yake bayyana damuwar sa, Hon. Yusuf ya buƙaci masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, da ƴan kasuwa, da su bayar da gudunmuwarsu don tallafa wa mutanen da abin ya shafa.

  Wani mazaunin ƙauyen Natsinta, Mas’udu Lawal ‘Sarkin Yashi’, ya alaƙanta wannan iftila’in da rashin wadatattun magudanan ruwa masu kyau a yankin.  Ya ƙara da cewa, “datsewar wata babbar magudanar ruwa ta kara ta’azzara tasirin ruwan saman da ya yi ɓarnar, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali,” in ji shi.

Kansila mai wakiltar mazaɓar Ƙusa, Shamsu Hassan, ya jaddada ruɗani da aka samu bayan faruwar lamarin. Inda ya ce, mazaunan da suka rasa matsugunansu na kokawa don samun mafaka domin rage raɗaɗin halin da  suke ciki.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa, Abdulrahman Ibrahim da Amina sun ba da labarin yadda asarar ta shafe su, inda suka ƙara da cewa ba gidajensu kaɗai suka rasa ba, har ma da muhimman kayyakinsu na amfanin yau da kullum, lamarin da ya ƙara dagula musu halin da suke ciki.

Jaridar Hausa Daily Post ta wallafa cewa, abin farin ciki, ba a sami rahoton asarar rayuka ba, ko da yake wasu mutane kaɗan sun sami raunuka a lokacin faruwar iftila’in.

Ɗan Madamin Katsina Hakimin Ɗaddara, Alhaji Usman Usman Nagoggo, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda jama’a ƙauyen ke cikin rudani.  Ya kuma yi kira ga jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su tausayawa al’ummar da abin ya shafa tare da aiwatar da matakan daƙile afkuwar irin haka nan gaba.

A yayin da al’ummar kauyen Natsinta ke kokawa kan wannan iftila’in da ya afku. Ana sa ran ci gaba da ƙoƙarin gyara yankin da abin ya shafa, tare da ƙudirin aniyar shawo kan wannan lamarin.

Sharhi/RadioTv

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *