Talala! kotu ta bada umarnin rufe asusun bankunan gwamnatin Kano


Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin dakatar da wasu daga cikin asusun gwamnatin jihar Kano a wasu bankunan kasuwanci guda 20 a Najeriya.

Alfijir labarai ta rawaito Mai shari’a I.E Ekwo ya bayar da wannan umarni ne a wata kara da masu shaguna a filin idi da kungiyar ‘yan kasuwa suka shigar a kan ruguza shagunansu da gwamnatin Kano tayi, wanda suka bayyana a matsayin haramtaccen matakin da gwamnati ta dauka a watan Yunin 2023.

Wadanda suka shigar da karar Sun hada da Alhaji Auwalu sai’du, Ifeanyi Nwobodo, Alhaji Sani Uba, Alhaji Abdullahi A. Idris, da wasu mutane 25 sun kai karar gwamnatin jihar Kano ne a matsayin masu bin bashi, har naira biliyan 30.

Umarnin kotun na kunshe ne a cikin daftarin hukuncin da aka bayar a ranar 28 ga Nuwamba, 2023 kuma aka bai wa manema labarai ranar Larabar nan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *