Daga Baba Usman Gama
Najeriya da Kuwait sun ƙulla yarjejeniyar fara zirga-zirgar jiragen sama.
’Yan Najeriya sun yi wa Majalisar Dokoki ta Kasa cikar kwari, suna zanga-zanga kan kisan Musulmi kimanin 90 da jirgin soji ya yi a wurin Mauludi a Jihar Kaduna.
Wasu matasa a Kano suka gudanar da zanga zangar neman Kotun Koli ta yi wa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf adalci a shari’arsa da APC.
Kungiyar dattawan Arewa ta ce Tinubu bai damu da matsalar tsaron Arewa da Najeriya ba.
ƴan bindiga sun sace muhimman takardun da ke tattare da kararrakin zaben gwamnan jihar Kogi sannan suka farmaki sakataren kotun saurarron karar zaben gwamna a Lokoja
An yi wa fursunoni 72 afuwa a gidajen yarin Zariya.
Dubban mazauna garin Abuja sunyi zanga-zanga domin ganin Nyesom Wike ya sauka daga kujerar da yake kai a yau.
’Yan bindiga sun harbe wani direba tare da sace mutane 8 da ke hanyarsu ta zuwa nadin sarautar Babban Limamin Bakarabonde a Masarautar Borgu a Jihar Neja.
Shugaba Putin ya isa Saudiyya domin tattaunawa da Bn Salman.
Ƙasar Saliyo ta kama wani mai gadin tsohon shugaban ƙasar kan juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Hezbollah da Isra’ila sun yi musayar wuta yayin da ake fuskantar tashin hankali a kan iyaka.
Pope golan Newcastle zai yi jinyar wata hutu.
Wani ɗan wasan kwallon ƙafa ya faɗi kasa ana cikin atisaye, rai ya yi halinsa a jihar Ogun.
Ingila za ta ci gaba da kula da iyalan magoya bayan Liverpool da ibtila’in 1989 ya rutsa da su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp