Daga Baba Usman Gama
Mai shari’a Musa Dattijo, Alkalin kotun koli, zai yi ritaya a ranar 27 ga watan Oktoba kamar yadda mai magana da yawun kotun kolin, Festus Akande ya sanar.
Zargin Kisa: Ana bincike kan rasuwar kwamishinan ’yan sanda a Borno.
Harin Boko Haram ofishin kwasatn a Geidam jihar Yobe ya yi sanadin mutuwar jami’i guda daya.
Shugaban kwamitin kafa rundunar tsaro ta Jihar Sakkwato, Kanar Garba mai ritaya ya yi murabus kwana 5 bayan Gwamna Aliyu ya kafa kwamitin.
An hallaka wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga a jihar Bauchi.
Dubun wasu malaman addinin Musulunci ta cika bayan kama su da jami’an ‘yan sanda su ka yi da zargin fille kan wani mutum a jihar Oyo.
Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Osun ya yi sanadiyyar mutuwar wasu matafiya 7.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kwankwaso ya bayyana shirinsa na taimakawa almajirai masu karatun allo, su yi karatun Boko a jihar Kano.
‘Yan bangar siyasa sun shiga kauyen Aja-Odi Agojoeju da ke karamar hukumar Ofu sun lallasa jagora a SDP Fasto Sunday Atabo inda sukayi masa dukan tsiya, har ta kai ya na kwance a gadon asibiti ko motsi bai iya yi a halin yanzu.
An yi wa shugabar wurin ibadar Yahudawa kisan gilla a kasar Amurka inda jami’an tsaro suka tsinci gawarta a caccaka mata wuka.
Red Cross ta yi kiran bai wa likitoci damar shiga Gaza.
Isra’ila ta ce ɗaya daga cikin tankokin yaƙinta ta harba makami cikin kuskure kan sojin Masar a kan iyakar Gaza.
Tsohon Fira Ministan Pakistan Nawaz Sharif da ya yi hijira ya koma gida.
Rukuni na biyu na manyan motoci dauke da kayan agaji sun shiga Gaza.
Jirgin Fadar Shugaban Turkiyya dauke da likitoci da magunguna da za a kai Gaza ya kama hanyar zuwa Masar.
Gidauniyar ba da agaji ta Majalisar Dunkin Duniya ta kai kayan abnci Gaza dan rage radadin iftila’in da ake fuskanta sanadiyyar yakin Falasɗinawa da Isra’ila.
Laliga: Girona ta sami nasara akan Almeria 5:2 a wasan yau.
Seria A: Roma ta sami nasara akan Monza da ci 1:0 a wasan yau.
Kano Pillars ta doke Rivers United da ci ɗaya mai ban haushi ana daf da tashi a wasan yau.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo