Gwamna Yahya Bello ya tsallake rijiya da baya a hanyarsa ta zuwa Abuja

FB IMG 1698006125997

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji suka yi a hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Alfijir labarai ta rawaito lamarin ya zo a lokacin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba cewar kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kingsley Femi Fanwo.

Ya ce an yi yunkurin kashe Gwamna Bello ne a tazarar kilomita kadan daga Abuja

An ce gwamnan yana kan hanyarsa ta zuwa wani aiki ne a Abuja daga Lokoka, babban birnin jihar Kogi, aka yi yunkurin kashe shi.

“Harin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023.

“Maharan da ke sanye da kakin soji sun tare ayarin motocin Gwamnan suka yi ta harbe-harbe a kan motarsa da sauran motocin da ke cikin ayarin.

Sai da jami’an tsaro da ke tare da Gwamnan suka shiga cikin gaggawa domin dakile shirin sojojin da ba a san ko su waye ba.

“Hare-haren sun kasance a wurare uku daban-daban, shingen karshe ya kasance a kusa da babban birnin tarayya Kwali da misalin karfe 4:20 na yamma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *