Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Lahadi 14/01/2024CE – 02/07/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya naɗa Minista Edun, Bagudu cikin kwamitin yi wa Shirin Inganta Rayuwar Masara Galihu garambawul

Hukumar EFCC ta sake waiwayar binciken halasta kuɗaɗen haram na wasu tsofaffin gwamnoni 12 da wasu ministoci da suka gabata, kuma adadin kuɗin ya haura naira biliyan 853.b.

Rundunar Sojoji ta fara bincike kan kisan gilla da ake zargin dakarunta sun yi wa wasu Fulani 11 a yankin Ladduga da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya ƙirƙiro da zauren dattawan Kano da zai riƙa bayar da shawarwari ga gwamnati.

Dandazon mutane sun tarbi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a Tashar Yari bayan nasarar da ya samu a kotun koli a ranar Juma’a.

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya ce kwana 7 ya kasa barci saboda jiran hukuncin Kotun Koli kan zabensa.

Gwamnan Zamfara yayi kira ga abokan hamayyar sa su zo a sa zamfara gaba domin ciyar da jihar gaba bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da nasararsa ta gwamna.

Gawuna yace fatan sa ga Gwamnan Kano Abba Kabir ya zama shugaba nagari mai adalci ga kowa

Ƴan bindiga sun bankawa motar da ta ɗauko kayan ɗakin amare uku wuta, sun kashe direba da yaron motar a kan hanyar Jibia-Batsari a jihar Katsina.

Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya roƙi ƴan bindigan da suka sace shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Ukum ta jihar, Gideon Haanongon da wasu mutum uku da su sake su ba tare da wani sharaɗi ba.

‘Yan cirani huɗu sun mutu a tekun Faransa.

An sako ma’aikatan gidan yarin da aka yi garkuwa da su a Ecuador.

An kashe sojojin Pakistan biyar a wani harin bam a lardin Baluchistan.

Isra’ilawan da Hamas ta yi garkuwa da ‘yan uwansu na znga-zanga.

Zaftarewar kasa ta hallaka sama da mutane 30 a Columbia.

‘Yan tawayen Houthi sun yi barazanar mayar da zazzafar martani bayan harin Amurka.

EPL: Everton da Aston Villa sun tashi 0:0 a wasan yau.

EPL: Manchester United da Tottenham sun tashi 2:2 a wasan yau.

AFCON: Nigeria da Equatorial Guinuea sun tashi 1:1 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *