Daga Baba Usman Gama
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kara tsaro yayin da ake shirin yin hukunci a shari’ar zaben Gwamna a garin Abuja.
’Yan ta’adda sun kashe Kwamandan jami’an tsaro a yankin Safana ta jihar Katsina.
Kotu ta dage shari’ar Rarara kan sukar tsohon Shugaba Buhari a jihar Nasarawa.
Reno Omokri ya zargi kungiyar kwadago da shiga yajin aiki saboda jam’iyyar LP ta fadi zabe a jihar Imo.
Najeriya ta soma bincike a kan soke bizar ‘yan kasar 264 da Saudiyya ta yi bayan isar su Jeddah.
Jam’iyyun adawa sun caccaki APC kan sakamakon zabukan Kogi, Imo da Bayelsa.
’Yan kwadago sun tsunduma yajin aiki.
Shugaban Hisba Daurawa ya ce Hukumar ta damu game da yadda bakin kananan ’yan mata ke kwararowa jihar da sunan shiga fim inda suka yi sansani a wurare daban-daban suna aikata badala.
Akalla mutum 32 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwalekwale a garin Ibbi da ke Karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.
Hukumar Tace finafinai ta Kano ta dakatar da Abdul Sahir da aka fi sani da Malam Ali Kwana Casa’in, tare da bai wa duk wanda ya sanya shi a fim sati 2 da suka gabata umarnin kai fim din hukumar don tantancewa.
‘Yan bindiga sun kashe mutane 70 a Burkina Faso.
kungiyoyin duniya irin su Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun gaza wurin shawo kan matsalolin duniya inda suka kara “ta’azzara” in ji Daraktan Watsa Labarai na Turkiyya Fahrettin Altun.
Majalisar mulkin soji ta Gabon ta sanar da cewa za a gudanar da zabe a kasar a watan Agustan shekarar 2025 bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Ali Bongo Ondimba.
Luiz Suarez ya dawo buga wa kasar sa ta Uruguay kwallo.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp