Kalaman ɓatanci ga Buhari: An maka Mawaƙi Rarara a kotu

FB IMG 1698531586245

Wani mazaunin garin Maraba da ke jihar Nasarawa, Muhammed Sani Zangina, ya shigar da kara kotu, inda ya zargi mawakin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu, wanda ake kira da Rarara, da tada hankalin jama’a.

Alfijir Labarai ta rawaito kwanakin baya Rarara, a yayin wani taron manema labarai kwanan nan a Kano, ya bayyana nadamar goyon bayan tsohon shugaban kasar, wanda ya zarge shi da lalata kasar kafin mikawa shugaba Bola Tinubu mulki.

A wata takardar ƙarar da kotu ta bayar ga City & Crime, wanda ya shigar da karar, ta hannun lauyansa, Muhammed Barde Abdullahi, ya ce matakin na Rarara na iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, da kuma kawo hargitsi, wanda ya saba wa sashe na 114 na kundin laifuffuka.

Sai dai kuma ba a yi zaman sauraron ƙarar, wacce aka shigar a wata kotun majistare dake zamanta a jihar Nasarawa ba a jiya Litinin 13 ga watan Nuwamba, saboda rashin halartar wanda ake kara.

Mai gabatar da kara na kotun ya bayyana cewa ba za a iya aika sammacin da kotun ta yi wa wanda ake tuhuma ba.

Daga nan sai Barista Abdullahi, ya nemi a canja hanyar baiwa wanda ake kara sammaci, inda kotun ta amince.

Alkaliyar kotun, Maryam Nadabo, ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Disamba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *