Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Laraba 15/11/2023 – 01/05/1445AH

best seller i2

Uwargidan Tinubu ta ba da tallafi ga mata da marayun da sojoji suka mutu suka bari.

Khalifa Muhammadu Sanusi II ya soki shekaru 8 na mulkin Muhammadu Buhari da yadda aka yi ta cin bashin CBN.

‘Yan sanda sun cafke wata amarya mai suna Amina Hassan a jihar Adamawa bisa zargin cinnawa gidan mijinta wuta bayan ya ƙi yarda ya sake ta.

Atiku ya nemi ƴan adawa su dunkule su ceto Najeriya daga “tsunduma mulkin kama-karya”.

Gwamna Dauda Lawal ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimi a jihar Zamfara baki daya don ceto jihar daga durkushewa har sannan ya kwace lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar don inganta harkar ilimi.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta soke belin da a baya aka bai wa tsohon Akanta Janar na Kasa, Ahmed Idris.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Jihar Benue ce kan gaba wajen safarar mutane a Najeriya.

An tsinci gawar wani matashin dan kasuwa da ake zargin sa ya rataye kansa a unguwar Sharada da ke Jihar Kano.

Gwamnan jihar Neja Umar Bago, ya bayyana cewa wasu ƴan kasuwan kasar Saudiyya za su gyara titin Minna-Bida nan ba da daɗewa.

Najeriya ta ce za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun naira har bayan Disamba.

Sojojin Mali sun kwace muhimmiyar tungar ‘yan tawaye ta Kidal.

Kungiyar Houthi a ranar Talata da dare ta bayyana cewa ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra’ila.

Shugabannin Musulmai sun ce laifin Ƙasashen Yamma ne ƙuncin da Gaza ke ciki.

Neymar na samun sauki bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwar kafa.

Manchester United na duba yiwuwar amsar tayi kan Casemiro, yayin da ƙungiyoyin Saudiyya ke kwaɗaitawa ɗan wasan makuɗan kuɗaɗe.

Chelsea da alama zata gabatar da tayi kan Victor Osimhen, a watan Janairu.

Juventus ta tuntubi Manchester United kan bata aron ɗan wasan Ingila, Jadon Sancho, a makon da ya gabata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *