An tsinci gawar wani mutum mai suna Saleh Abdullahi mai shekaru 35 a duniya bayan ya rataye kansa a wani daki da ke unguwar Sharada a Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito an tsinci wata rubutacciyar takarda, da aka bude sai aka ga an rubuta: “a yi hakuri.” Amma sauran ba a iya karanta su ba, an ce yana zaune ne a gidan dan uwansa, Idris Hamisu.
Hamisu ya bayyana cewa, “Na dawo daga sallar asuba, na tashi matata domin ta yi wa ‘ya’yanmu abinci, kuma tana neman ashana domin ta kunna wuta amma babu.
Ta tuna Salisu yakan yi amfani da turaren gida. Da ta aiko yaronmu ya karbo ashana, sai yaron ya gan shi a rataye, sai ya koma da gudu yana ihu wai wani ne ya rataye Yaya Saleh. Sai na garzaya daki na ga gaskiya ne”.
Da aka tambaye shi ko yana da wata matsala shi marigayin, sai ya ce, “Ba mu sami wata matsala ba. Abin da na sani shi ne cewa a kwanakin nan ya damu, kuma a matsayinmu na ’yan kasuwa, muna jin haka idan kasuwa ta lalace.
‘’Mu ’yan kasuwa ne kuma muna cinikin kayan daki, amma Saleh wani lokaci ya kan sayo da sayar da tsofaffin kayan.
“Ya nuna alamun damuwa a kwanakin nan saboda ya karbi kudi a hannun wani ya siyo kayan da kudinsu ya kai N400,000 a Rijiyar Zaki daga hannun wasu mutane suka kai shi gidan inda suka ajiye kayan suka ce ya dawo wata rana ya kai su.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Da ya nemi lambar wayarsu, sai suka ce tunda ya ga gidan zai iya dawowa kowane lokaci, kuma da ya koma daga baya bai samu gidan ba.
Abin da ya jawo masa damuwa kenan domin kudin ba nasa ba ne kuma mai shi ya matsa masa ya biya shi.”
Babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan kan lamarin izuwa yanzu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp