Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Laraba 03/01/2024 – 21/06/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin jihar Kano za tayi wa ma’aikatanta Karin dubu 20 ‘yan fansho kuma karin dubu 15 saboda halin da ake ciki.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce har yanzu Baffa Bichi ne Sakataren Gwamnatin Kano kuma babu wata rigima a tsakaninsu.

Dakarun rundunar Sibul Difens NSCDC sun kama manyan motocin 2 cike da shanun sata a karamar hukumar Tsafe dake jihar Zamfara.

An yi ƙazamin artabu tsakanin ƴan banga da ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ya sanya ƴan bindiga sama da 40 sun sheƙa barzahu.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya yi barazanar daina tallafa wa kungiyar kwallon kafar Gombe United saboda rashin katabus.

An kama buhunan takin zamani 600 na sata a Kaduna.

Turkiyya ta tsare wasu mutane 33 bisa zargin shirin sace mutane da kuma yin leken asiri a madadin hukumar leken asirin Isra’ila.

Trump ya daukaka kara kan hukuncin hana shi shiga zaben jihar Maine.

Hezbollah da Hamas sun sha alwashin daukar fansar kisan al-Arouri.

EPL: West Ham da Brighton sun tashi 0:0 a wasan jiya.

Laliga Rayo Vallecano sun sami nasara akan Getafe da ci 2:0 a wasan jiya.

Laliga: Valencia ta sami nasara akan Villarreal da ci 3:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *