An Sako Shugaban Karamar Kukumar Akwanga Da Aka Sace Bayan Biyan Miliyoyi

IMG 20240102 113247

An yi awon gaba da shugaban karamar hukumar tare da abokinsa da wasu mutum biyu a daren Litinin.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban Karamar Hukumar Akwanga da aka sace a Jihar Nasarawa, Safiyanu Isah Andaha, tare da wasu mutum uku sun kubuta bayan an biya kudin fansa miliyan 10.

An sace shugaban tare da abokinsa, Adamu Custom da wasu mutum biyu, a kan titin Akwanga zuwa Andaha a daren Litinin.

Wani makusancin shugaban karamar hukumar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa an sako duk wadanda abin ya shafa ne bayan an biya kudin fansa.

Majiyar ta ce โ€œAn sake su ne a daren Talata da misalin karfe 9 a bayan wani gidan mai da ke kan titin Bayan Dutse, kuma an biya kudin fansa Naira miliyan 10.โ€

Majiyar ta ce shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa maharan suka ci zarafinsu lokacin da suka sace su.

Aminiya ta samu labarin cewa jim kadan bayan sakin su aka garzaya da su zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), da ke Keffi don duba lafiyarsu.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *