Daga Baba Usman Gama
Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Zacch Adedeji a matsayin shugaban hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS).
Ministan harkokin wajen Najeriya ya karɓi baƙuncin jakadan Falasɗinawa.
Akalla mutum 12 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Sanatan Gombe ta Arewa, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, ya buƙaci a dakatar da biyansa kudaden fansho da alawus-alawus da ya kamata a biya shi a matsayinsa na tsohon gwamna.
Akalla mutum 16 sun mutu yayin da wasu 4 suka jikkata sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai a Karamar Hukumar Geidam ta Jihar Yobe.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja ta cafke wata yarinya kan zargin hallaka lacrara a jihar.
An halaka ƴan sanda 3 a wani hari da aka kai kan shingen binciken ababn hawa akan hanyar Funtua zuwa Tsafe ta jihar Zamfara.
Majalisar Dinkin Duniya ta yiwa Benjamin Netanyahu martanin cewa kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza dole ne ba zabi ba.
Harin roka ya jikkata mutum huɗu a Isra’ila, in ji hukumar agaji.
Masu neman a tsagita wuta a Gaza sun tsayar da taron Majalisar Dattawan Amurka.
Isra’ila ta ce an kashe sojojinta biyu a harin da suka kai Zirin Gaza.
An gudanar da gasar kyau ta mata da maza zabiyoyi a Kudancin Afirka.
Manchester United ta tura wakilai domin nazartar ɗan wasan Portugal mai tsaron raga Diogo Costa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp