Daga Baba Usman Gama
NDLEA ta ce ta gano gonar tabar wiwi a jihar Sokoto.
Gwamnan jihar Kano, ya bankado wani sito da aka boye kayan tallafin abinci a Unguwar Sharada da ke birnin Kano.
Shugaban riƙo na jam’iyyar PDP, Umar Damagum, ya ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ƙarƙashin jagorancinsa ba zai dakatar ko korar duk wani mamban jam’iyyar mara biyayya ba.
Wani mutum ya kashe kawunsa kan zargin maita a Adamawa.
An samu tashin gobara a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke a babban birnin tarayya Abuja.
Jam’iyyar APC ta sake sabon kamu bayan sanatoci biyu daga jihar Anambra sun sauya sheka zuwa jam’iyyar.
KANJAMAU: Sama da mutum 4000 da ke ɗauke da cutar a Kano na amsar magani kyauta a asibito- cin jihar.
Wani ma’aikaci a Bolorunduro, Karamar Hukumar Ondo ta Gabas a Jihar Ondo, da aka ce sunansa Mathew ya fadi ya mutu a ofishinsa.
Rasha na ƙara dakarunta a yaƙi da Ukraine mai samun goyon bayan Nato.
Kwamitin tsaro na MDD ya cire wa Somaliya takunkumin shigar da makamai.
Nijar da Burkina Faso sun janye daga kawancen G5 Sahel na Faransa kan yaki da ta’addanci.
Barcelona za ta ba Robert Lewandowski damar tafiya a kakar wasa mai zuwa.
Real Madrid na son ɗauko tsohon ɗan wasanta Xabi Alonso zuwa Bernabeu a matsayin sabon kocinta wanda ke jagorantar Bayer Leverkusen.
EPL: Newcastle ta sami nasara akan Manchester United da ci 1:0 a wasan jiya.
Laliga: Real Madrid ta sami nasara akan Granada da ci 2:0 a wasan jiya.
Seria A: Ac Milan ta sami nasara akan Frosinone da 3:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp