Tsohuwar ta yi ta ihu tana neman taimako. Bayan haka, na yi ta dukanta har sai da ta fadi ta mutu.”
Alfijir labarai ta rawaito Wata kotun majistare da ke zamanta a Akure a jihar Ondo ta gurfanar da Mubarak Akadiri bisa zargin kashe Sidikat Adamolekun, wata tsohuwa mai shekaru 62 bayan tayi ritaya.
Matashin mai shekaru 18, wadda dan aikin gidan ne, ana tuhumarsa ne da kashe Adamolekun bayan ta kama shi yana satar wayarta, wanda kudinta ya kai N66,000.
A lokacin da ake tuhumar sa a gaban kotu a ranar Juma’a, matashin wanda ake zargin ya amsa laifin kashe matar ta hanyar yi mata dukan tsiya da katako.
Ya bayyana cewa, “Kamar yadda na saba na je gidan ina aiki, daga baya na dawo na sace wayar ta Samsung. Duk da haka, ta kama ni bayan na sace wayar. A ƙoƙarin tserewa, na yi amfani da wani katakol na buga mata ka.
Tsohuwar ta yi ta ihu tana neman taimako. Bayan haka, na yi ta dukanta har sai da ta fadi ta mutu.”
Yayin da kotun ta gama sauraron wanda ake zargin da laifin kisan kai, dan sanda mai shigar da kara, Simon Wada, ya roki kotun da ta tsare wanda ake kara a gidan yari na Olokuta har zuwa lokacin da za a ba shi cikakken bayanai daga Daraktan kararrakin jama’a (DPP).
Alkalin kotun, Damilola Sekoni, ya amince da bukatar mai gabatar da kara, inda ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a cibiyar har zuwa sakamakon shawarar da DPP ta bayar.
An dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga Maris, 2024.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp