Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Juma’a 10/11/2023 – 26/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Karamin ministan tsaron, Bello Matawalle, ya ce gwamnatin da ta gabata ba ta dauki batun rashin tsaron ƙasar nan da muhimmanci ba.

Zaben Gwamna: An tura jami’an tsaro dubu 40 jihar Kogi.

Kwastam ta kasa ta canza lissafin da ta ke amfani da shi wajen karbar kudin shigo da kaya daga kasashen ketare.

Limamin cocin Katolika na Sokoto, Rabaran Mathew Kukah, ya bayyana wani abin mamaki game da tsohon shugaba Buhari. yace ya kadu da jin yadda ministocin Buharin suke magana akan sa

Dakarun soji da ke atisayen Safe Haven sun samu nasarar kamo wanda ake zargi da kashe Adamu Gabdo, sarkin al’umar Fulani makiyaya a Filato.

Rundunar soji ta sake sabon gargaɗi bayan gano wasu gurɓatattu na shirin yin shigar sojoji a zaɓen gwamna da ke tafe a jihohi uku.

Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata ta kammala shirye-shiryen gurfanar da Shugaban Hukumar karbar Korafe-Korafe ta Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado a gaban kotu.

Dan takarar gwamnan Kogi na APC Dino Melaye, ya bayyana cewa idan ya zama gwamna zai gina Otel Otel a saman ruwa a jihar.

Gwamna jihar Akwa Ibom ya amince da biyan ma’aikatan jiharsa albashin watan 2 domin su yi shagalin kirsimeti.

Atiku Abubakar da tawagarsa sun isa jihar Kogi domin halartar gangamin kamfen Dino Melaye.

Sojojin Isra’ila sun ce bidiyon ‘yan ƙasarta da ake riƙe da su alamun suna raye ne.

Ramaphosa ya umarci sojojin Afirka ta Kudu su hana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Majalisar Wakilan Madagascar ta buƙaci a dakatar da zaɓen shugaban ƙasar.

Isra’ila za ta fara ‘dakatawa’ da kai hari na tsawon awa hudu kowace rana a Gaza.

Saudiya za ta tallafa wa kasashen Afrika don rage bashin da ke kansu.

‘Yan tawayen Colombia sun sako mahaifin Luis Díaz.

Magoya bayan Man United za su yi zanga-zanga a Old Trafford.

Europa: Brighton ta sami nasara akan Ajax da ci 2:0 a wasan jiya.

Europa: Toulouse ta sami nasara akan Liverpool da ci 3:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *