Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta Code of Conduct Bureau, ta sanar cewa ta kammala dukkanin shirye-shirye na gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da aka fi sani da ‘Anti Corruption’ a gabanta.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar ta sanar cewa a ranar Alhamis ta makon gobe 16 ga Nuwamba ne hukumar za ta gurfanar da Barr Muhyi.
Wata majiya daga hukumar ta ce za a gurfanar da Barr Muhyi ne bisa zargin wasu laifuka na gaza mika mata rubutaccen bayani game da kadarorin da ya mallaka da sauran laifuka.
A wani sammace da Magatakardan hukumar ya aike wa shugaban hukumar, an umurce shi da ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tuhume-tuhume guda 10.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp