Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin sa ta na kokarin ganin ma’adanai sun zama mafi girman hanyan samun kudin shiga.
‘Yan Majalisa sun cire Naira biliyan 5 da Tinubu ya ware don sayen jirgin ruwan shaƙatawa, sun narka kuɗin cikin kasafin basussukan ɗaliban jami’o’i.
Majalisar wakilai ta fara binciken yadda aka kashe kuɗin tallafin Korona.
Wani jirgin ruwa ya kife ɗauke da fasinjoji a karamar hukumar Fufore da ke jihar Adamawa
zuwa yanzu an ciro gawawwaki 6, yayin da aka ceto mutane 14 da ransu.
Wata Kotu a Abuja ta bada umarnin gaggauta sakin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
‘Yan sanda sun kashe dan bindiga, sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su a filato.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zargi shugaban kungiyar kwadago ta kasa Joe Ajaero, da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar.
Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin ƙaramar Kotu wanda ya ayyana zaben ɗan majalisar Birnin Kudu/Buji a matsayin wanda bai kammalu ba.
Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a unguwar Mpape da ke Abuja, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu.
Idan abubuwa sun tafi daidai, NNPCL zai rika saidawa Aliko Dangote danyen mai a farashin kasuwa.
‘Yan Democrat sun damu kan yiwuwar rasa kuri’un Musulmai a Amurka saboda goyon bayan Isra’ila da Biden ke yi.
Kungiyar Hizbullah ta Labanan ta kai hari wurare 19 lokaci guda a Isra’ila.
Daruruwan ’yan Ghana sun gudanar da zanga zangar nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a titunan babban birnin kasar Accra.
Harin roka da Hamas ta kai Isra’ila ya jikkata mutum biyu.
Jami’an tsaro sun kama gungun ‘yan ta’adda a yankin Arlit mai iyaka da Nijar da Aljeriya.
‘Yan bindiga sun sace malaman makaranta a jihar Tilabery a Nijar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp