Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Mutane 24 Bisa Aikata Muggun Laifuka A Kano

FB IMG 1668778250057

Kamishinan Yan sandan Jihar Kano CP Muhammad Hussain Gumel ya Jinjinawa jami’an sa bisa sadaukarwa wajen yaki da masu aikata laifuka Daban-daban.

Alfijir Labarai ta rawaito Rundunar Yan sandan Jihar Kano ta samu nasarar kama ƙarin wasu mutane 24 da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi da sauran laififfuka Kasa da mako Guda.

Wananan Nasarar na daga Cikin Umarnin da Babban Sifetan Yan sandan Nigeria kayode Egbetukun ya bayar wajen gudanar da tsarin inganta mu’amala tsakanin ƴan sanda da al’umma wajen Dakile ayyukan bata gari dake tsakanin alumma

A ranar 2 ga watan da muke ciki sashin yaki ANTI DABA karkashin Jagorancin O/C Anti-Daba, SP Hussaini Gimba ya samu nasarar kama masu laifin Kimanin 24 Dake Ta’ammali da miyagun kwayoyi

Ta Cikin wata Sanarwa Da Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar yace, za a mika manyan dilolin kwayar ne ga hukumar yaki da Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA. Domin Cigaba da Fadada Bincike

Kamishinan Yan sandan Jihar Kano CP Muhammad Hussain Gumel ya Jinjinawa jami’an sa bisa sadaukarwa wajen yaki da masu aikata laifuka Daban-daban.

Ya kuma buƙaci al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da baiwa Rundunar haɗin kai da goyon baya domin samun nasarar ayyukan ta wajen daƙile ayyukan bata gari.

📸SP Kiyawa
📸SP Kiyawa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *