Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin tarayya ta ce nan da ‘yan watanni kadan sabon tsarin albashi zai soma aiki a kasar.
‘Yan sanda da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga sama da 50 a Taraba.
Majalisar dattawa ta ce bincikenta ya nuna mata an karkatar da kudin tallafin da bankin CBN ya ba kamfanoni.
Gwamnatin jihar Kano za ta fara biyan giratutin ma’aikatan da su ka yi ritaya daga aiki kamar yadda ta dauki alkawari.
Gwamnatin Kaduna ta jaddada matsayinta na yin dandaka ga duk namiji ko macen da aka kama ya aikata fyade a jihar.
Al’ummar Musulmi a jihar Plateau sun karyata jita-jitar cewa Gwamna Cale Muftwang na jihar Plateau na nuna musu wariya.
OPEC ta rage man da Najeriya zata dinga hakowa a shekara mai zuwa.
‘Yan uwan hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum sun ce ba su ji labarin halin da yake ciki ba tun ranar 18 ga watan Oktoba.
Isra’ila zata saki Falasdinawa 30 yayin da ita kuma Hamas za ta saki Isra’ilawa 10 a kwana na 7 na yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakaninsu.
Manchester United na tattauna da ɗan wasan baya na Romania da Genoa Radu Dragusin, mai shekara 21.
Europa League: Liverpool ta sami nasara akan Lask da ci 4:0 a wasan jiya.
Europa League: Villarreal ta sami nasara akan Panathinaikos da ci 3:2 a wasan jiya.
Europa League: Brighton ta sami nasara akan Athens da ci 1:0 a wasan jiya.
Europa League: Marseille ta sami nasara akan Ajax da ci 4:3 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp