Wata babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan Sarkin Fulanin jihar Kwara, Alh Usman Adamu, da dan uwansa, da wani Gidado Idris, bisa samun su da laifin hada baki na yin garkuwa da wani bawan Allah.
Alfiir labarai ta rawaito an yanke wa mutanen uku hukuncin daurin rai da rai a ranar Alhamis.
An zarge su da yin garkuwa da Abubakar Ahmad kuma ana zarginsu da karbar kudin fansa naira miliyan daya kafin a sake shi bayan shafe kwanaki 20 a hannunsu.
Lamarin satar mutumin ya faru ne a tsakiyar shekarar 2022.
Daraktan shigar da kara na jihar Kwara (DPP), Idowu Ayoola, ya gabatar da wadanda ake tuhuma uku a gaban kotu bisa zargin hada baki wajen yin garkuwa da wani mutum.
A hukuncin da ta yanke, Mai shariโa Adenike Akinpelu, ta ce mutanen uku duk sun amince da aikata laifi, inda ta ce ko a jikinsu basu yi da nasanin abinda suka aikata ba.
Ta ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun kama wanda ya shigar da jara suna masu ikirarin cewa shi mai garkuwa da mutane ne domin karbar kudi daga gare shi.
Tashar Liberty TVR
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐๐
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp