Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 24/08/2024CE – 19/02/1446AH

B2

Shugaba Tinubu ya sha alwashin amfani da damar da yake da ita wajen ci gaba da samar wa sojoji kayan aiki da makamai, domin gudanar da ayyukansu.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnonin Bayelsa, Imo da Kogi.

Gwamnatin tarayya ta bankaɗo mutum 21,600 da ke amfani da shaidar kammala digiri na boge a ƙasarnan.

An kubutar da dalibai 20 na Jami’ar Maiduguri da Jos na kiwon lafiya da ƴan bindiga suka sace a jihar Benuwai.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya ce gwamnati ta shirya ganawa da kungiyar malaman jami’o’i a ranar Litinin mai zuwa.

Gwamnatin tarayya zata karbo bashin dala milyan 500 daga Bankin duniya don bunkasa Ilimi da kiwon lafiya.

Hukumar haraji ta nemi a samar da dokar sa ido a kan ƴan Kirifto.

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya isa birnin tarayya, Abuja domin halarta taron masu riƙe da sarautun gargajiya da za’a gudanar a Abuja.

Babban lauyan gwamnatin Venezuela ya ce Gonzalez zai bayar da shaida a kotu.

Indiya da Ukraine sun alƙawarta mutunta juna.

Fursunoni sun kashe jami’an gidan yari huɗu a Rasha.

Juventus na tattaunawa da Manchester United a kan Jadon Sancho.

Manchester United ta amince da kwangilar sayen ɗan wasa, daga Guidars FC, Sekau Kone.

Laliga: Celta Vigo ta sami nasara akan Valencia da ci 3:1 a wasan jiya.

Laliga: Villarreal ta sami nasara akan Sevilla da ci 2:1 a wasan jiya.

Bundesliga: Leverkusen ta sami nasara akan M’Gladbach da ci 3:2 a wasan jiya.

Lig 1: PSG ta sami nasara akan Montpellier da ci 6:0 a wasan jiya.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *