Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya amince naɗin Mr. Shaakaa Chira, a matsayin sabon Babban mai Binciken Kuɗi na Ƙasa.
Gwamnatin Najeriya za ta gina rukunin gidaje 34,500 a faɗin ƙasar.
INEC tace korar kararrakin zaɓe 900 da kotu ta yi ya nuna cewa sun gudanar da sahihin zaɓe.
‘Yan Najeriya sun koka bisa shirin ciyo bashin sama da dala biliyan guda.
Shugaba Tinubu ya amince da kafa wasu sabbin jami’o’in tarayya guda 7 a fadin kasa.
Majalisar Najeriya ta bayyana shirin sayen zabga zabgan motoci ga dukkan dattawan majalisar da mambobin tarayya, domin su ji daɗin karakainar zuwa wurin aiki.
Gwamnan jihar Zamfara ya zargi Ministan tsaro Matawalle da yin walle-wallen biliyoyin kuɗaɗe da sunan kwangilar gina filin jirgin sama a jihar.
Gwamnatin Sakkwato ta ɗauki nauyin karatun ɗalibai 15 zuwa ƙasar waje domin su yi karatu.
NNPC ya ce an samo tashin karamin gobara a matatar mai da ke Warri jihar Delta.
Masu harkar canjin kuɗi na kokawa kan faɗuwar darajar Naira.
Jami’an Isra’ila sun tabbatar da sakin Amurkawa 2 da Hamas ta yi garkuwa da su.
Biden ‘ya yi matukar farin ciki’ da sakin Amurkawa biyu da aka yi garkuwa da su.
Shugaban majalisar tarayyar kasashen turai ya nemawa masar taimako saboda rikicin Gaza.
Ministan Faransa Darmanin na musayar yawu da Karim Benzema a kan rikicin Gaza.
Laliga: Osasuna ta sami nasara akan Granada da ci 2:0 a wasan jiya.
Bundesliga: Dortmund ta sami nasara akan Werder Bremen da ci 1:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo