Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga watan Disamban 2023 a matsayin hutun bikin Kirsimeti.
Yayin da rikicin jihar Rivers ke kara kamari, dattawan jihar sun maka Shugaba Tinubu a Kotun sun shigar da karar ne a kotun saboda tilasta Gwamna Fubara na jihar da shiga yarjejeniya da Nyesom Wike.
An gurfanar da wani matashi a kotu a Kano bisa zargin kashe abokinsa saboda naurar sauraren sauti ta Bluetooth.
‘Yan sandan jihar Enugu sun kama wani tsohon kansila a karamar hukumar Enugu ta Kudu bisa wasu laifuka da suka hada da shiga kungiyar asiri da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wata matar aure bisa zarginta da kisan wani matashi da suke zaune a gida daya.
Dan majalisa daga Kano mai wakiltar Wudil da Garko ya ce tun shekarar 2014 DSS suka kama wani Isa Umar, har yau dai babu labarins ya bukaci a sakeshi.
Mahaifiyar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ta riga mu gidan gaskiya.
An kama tsohon minista a Kenya kan zargin cin hanci.
Faransa ta haramtawa ɗaliban Najeriya tafiya da Iyalensu.
Luiz Suarez ya koma Inter Miami ta Amurka da taka leda.
Manchester United na nazarin zawarcin dan wasan Sevilla El Nesyri saboda ɗan wasan da suke hari, Serhou Guirassy daga Stuttgart ya fi son tafiya Tottenham.
FIFA Club World Cup: Manchester City tayi nasarar daukar kofin bayan cin Fluminense 4:0 a wasan jiya.
Kocin Liverpool Jurgen Klopp yace shirin samar da gasar Super League ya girgiza EUFA matuka.
EPL: Brighton da Sheffield United sun tashi 1:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
Nohttps://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp