Daga Baba Usman Gama
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami shugabannin hukumomi shida da ke karkashin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama.
Gwamnatin tarayya ta tsaida albashin wasu ma’aikatanta biyo bayan binciken da aka gudanar a watan Oktoba.
Ministan Tsaro Badaru ya ce ma’aikatarsa za ta yi amfani da karin kasafin kudinta na 2023 da wani bangare na kasafin 2024 domin kawo karshen ta’addanci a Najeriya.
Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya ce za su kwato duk wasu kudade da kadarorin Najeriya da aka sace aka boye a kasashen waje.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta tallafawa ‘yan banga da Babura 730 domin tunkarar barayin daji.
EFCC ta bayyana cewa tana neman tsohon ministan makamashi da ƙarafa na kasar, Olu Agunloye, ruwa a jallo.
Rundunar ’yan sandan Kano ta ce bata-gari ne suka cinna wa sakatariyar Karamar Hukumar Gwale wuta, tare da jifa da duwatsu.
Hukumar Aikin Hajji ta dakatar da rabon kujeru ga kamfanonin jirgin yawo.
Sojojin Najeriya sun musanta zargin wani hafsa da sayen gida da kudin almundahana a Amurka.
Sarkin Salman bn Abdulaziz na kasar Saudiyya ya nada Yarima Salman bn Sultan bn Abdulaziz Gwamnan Madina.
Amurka na so ta ci gaba da kawance da sojojin Nijar kan sha’anin tsaro amma dole su hanzarta kama hanyar barin mulki.
Majalisar Wakilan Amurka za ta kada kuri’ar amincewa da bincike don tsige Biden.
UCL: Royal Antwerp ta sami nasara akan Barcelona da ci 3:2 a wasan jiya.
UCL: Atletico Madrid ta sami nasara akan Lazio da 2:0 a wasan jiya.
UCL: Newcastle tayi bankwana da gasar bayan rashin nasara a wanen Ac Milan da ci 2:1 a wasan jiya.
UCL: Manchester City ta sami nasara akan Zvezda da ci 3:2 a wasan jiya..
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp