Takaitattun Labaran Daniya Na Yammacin Talata 28/11/2023 – 14/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin tarayya za ta karɓi rancen dala biliyan ɗaya don cike gibin kasafin kudi.

Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari shugaban kamfanin NNPC.

An sake mayar da Emefiele kurkuku zuwa Janairu 2024 saboda gaza cika ƙa’idar beli.

Mayakan boko haram sun hallaka masu aikin gawayi 11 a jihar Barno.

Ƴan Najeriya sun kashe N2.6tn wajen sayen katin waya da data a cikin watanni tara.

Wasu ‘yan bindiga sun harbe ‘yan sanda biyu da wani matashi har lahira a mahadar Ahiara da ke Karamar Hukumar Ahiazu Mbaise a Jihar Imo.

Wani riƙaƙƙen ɗan daba ya miƙa kansa ga ƴan sandan Kano.

Mutum 2 sun mutu yayinda wasu mutum 8 suka jikkata a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma a ƙaramar hukumar Suru ta jihar Kebbi.

Kimanin dalibai 433 a cikin 836 da suka karanta fannin likitanci a jami’o’in ƙasashen waje sun faɗi jarrabawar samun lasisi da cibiyar yi wa likitoci rijista a Najeriya (MDCN) ta shirya.

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) a Saudiyya, ta tarbi Hajiyar Najeriya ta karshe, Kuburat Motolani Oloruntunmi da rashin lafiya ta tsare a kasar.

‘Yan ta’adda sun kai mummunan hari kan rundunar Sojin Burkina Faso.

Libya ta kora bakin haure sama da 200 zuwa kasashen Nijar da Chadi.

An ceto ma’aikatan haƙar ma’adanai 41 da suka yi kwana 17 a ƙarƙashin ƙasa a Indiya.

Wata kotu a Kenya ta ayyana harajin gidaje da cewa ba ya kan doka.

Masu haƙar ma’adinai 11 sun mutu a wani hatsari a Afirka ta Kudu.

An fara shari’ar matar tsohon shugaban kasar Zambia Esther Lungu.

Ambaliyar ruwa ta mamaye yankuna 38 na kasar Kenya.

Najeriya na duba yuwuwar sallamar kocin Super Eagles.

A yau Talata za a dawo Gasar Champions League bayan gajeran hutun da aka je.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *