Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai bar ƙasar a ranar Laraba zuwa birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron sauyin yanayi na COP28.
Alfijir labarai ta rawaito a wata sanarwa da ta fito daga hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar kan hulɗa da jama’a, Ajuri Ngelale, a yau Talata, ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a taron wanda zai gudana tsakanin ranakun 1 da 2 ga watan Disamba.
Bayanin da shugaba Tinubu zai gabatar lokacin taron zai mayar da hankali ne kan matsayar Najeriya game da sauyin yanayi, musamman abin da ya shafi amfani da makamashi maras gurɓata muhalli da kuma samar da kuɗi kan ayyukan daƙile ɗumamar yanayi.
Ana sa ran kuma shugaban na Najeriya zai yi amfani da damar wajen neman ƙasashen da suka ci gaba da su ƙara tallafa wa ƙasashe masu tasowa wajen yaƙi da sauyin yanayi.
Haka nan Tinubu zai yi amfani da lokacin taron wajen ganawa da masu ruwa da tsaki da nufin janyo ra’ayinsu wajen zuba jari domin samar da aikin yi a Najeriya.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp