Ta’addanci! Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma tare da jama’arsa

IMG 20240102 113247

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa Safiyanu Isah.

Alrijir labarai ta rawaito an yi garkuwa da Isah ne a daren Litinin, 1 ga watan Janairu, 2024, a kauyen Ningo, dake kan titin Akwanga-Andaha.

Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kamal Dauda Rija, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an sace shi ne tare da wasu, ciki har da wani fitaccen mai bayar da agaji a karamar hukumar, Adamu Umar, wanda aka fi sani da Maccido.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel, da jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sauran hukumomi, sun yi gaggawar fara farautar wadanda suka yi garkuwa da su domin ganin an sako wadanda aka sace.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *