Ta’addaci! Jerin Sunayen ’Yan Daba 13 Da Ake Nema Ruwa A Jallo A Kano

FB IMG 1704087088969

’Yan sanda sun fitar da jerin sunayen manyan ’yan daba 13 da suke farauta a birnin Kano

Alfijir labarai ta ruwaito Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta bayyana sunayen wasu gaggan ’yan dana 13 da suka addabi garin Kano a baya-bayan nan.

Rundunar ta sanar da neman su ruwa a jallo sakamakon zargin hannunsu a dawowar dabanci da kwacen waya musamman a yankunan kananan hukumomin Dala Gwale da kuma Birni.

Sanarwar da kakakin rundunar, Haruna Abdullahi Kiyawa ga fitar ta umarci ’yan daban da suka kai kansu hedikwatar rundunar da ke Bompai, tun kafin su shiga hannun jami’an rundunar da ke farautar su.

Wadanda ake neman su ne:

Halipa Here

Sheye Injiniya

Yusuf Ilu

Walidi Auwalu Kapinta

Tijjani Rattagu

Agiri Balarabe

Dan Kasuwa

Dan Makare

Nasuru Madadi

Hali Pan Pan

Jamilu Piye

Saiyid Zawai

Inyasi

Kiyawa ya ce rundunar ta tura karin jami’anta sassan jihar a matsayin wani bangare na matakan ta dauka na murkushe ayyukan bata-gari da kuma tabbatar da doka da oda a Kano.

Don haka ya bukaci wadanda suka san ’yan daban da ake nema da su sanar da su cewa su kai kansu, kar su gamu da fushin rundunar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *