Ta Faru Ta Kare: Gwamna Yusuf ya karbi rahoton kwamatin binciken kwamishinan sufuri

FB IMG 1754313667956

Gwamnatin jihar Kano ta sallami kwamishinan kula da harkokin sufuri na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Namadi Dala daga aikinsa nan take.

An dauki wannan matakin ne bayan gabatar da rahoton da gwamna Yusuf ya kafa ka kan binciken kwmashinan na sufuri da aka zarga da taka rawa wajen karbar belin dilan kwaya a Kano Danwawu Fagge daga babbar kotun jiha.

Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin Kano.

Sakataren gwamnatin Kano yace kamar yadda gwamna Yusuf yake takatsantsan wajen daukar mutum aiki a kowanne mataki a gwamnati haka yanzu ma , idan an samu matsala da mutum sai an bi a hankali wajen daukar mataki domin yiwa kowanne bangare adalici, inda ya ce ba batu ne na gaggawa ba.

“Mun san cewa abin ya taba ran mutanan kano,kowa ya tofa albarkacin bakinsa ,mai kyau da akasin haka”,Inji Sakataren gwamnatin Kano

Ya tabbatar da cewa zai mika rahoton ga gwamna Abba Kabir Yusuf kuma nan gaba zai sanar da matsayin gwamnatin Kano akan lamarin.

A nasa jawabin shugaban kwamatin binciken da gwamna ya kafa, Barista Aminu Husaini yace sun tuntubi kowanne bangare kafin gabatar da rahoton.

Hukumomin da aka tuntuba a cewarsa sun hada da DSS da NDLEA da Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA da sauran masu ruwa da tsaki.

Haka kuma Barista Aminu yace, sun gayyaci shi kansa kwamishinan na sufuri domin ji daga gareshi, kuma ya bada hadin kai.

Haka zalika, kwamatin yace ya karbi dukannin takardun shari’a daga babbar kotun jihar Kano, domin yin nazari akansu.

Yace sun mika rahoton domin gwamna Yusuf ya dauki mataki na gaba.

Yan kwamanti sun godewa gwamna Yusuf a bisa yadda bai taka rawa ba ko yin katsalandan a aikin nasu.

A baya dai kwamishinan na Sufuri ya musanta dukannin zarge zargen da akeyi masa harma ya nemi afuwar jama’ar Kano.

A karshe Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk ya rushe kwamatin saboda gama aiki da yayi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *