Son Banza! Wani Magidanci Ya Ragargaza Matarsa, A Karshe Ya Kasheta.

Alfijr ta rawaito wani magidanci mai suna Segun Omotosho Ebenezer, ya lakadawa matarsa ​​Bukola duka, wanda dalilin wannan dukan ya kashe ta har lahira.

Wani bincike ya tabbatar da dalilin faruwar hakan, ya samo asali ne saboda ta ki mika masa makarantar firamare da ta gina da sunanta.

A cewar rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, wanda ake zargin da marigayiyar sun yi ta cece-kuce a kan kadarorin kafin ya lakada mata duka ta mutu.

A wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar a ranar Litinin din da ta gabata sun ce an kama mutumin ne bayan da ya gudu a lokacin da ake sauraren karar muryar da matarsa ​​ta aika wa ‘yan uwanta a kan batun.

Wanda ake zargin dai ba a sani ba, marigayiyar ta aika da sakon murya ga ‘yan uwanta, inda ta sanar da su cewa mijin nata ya yi amfani da wani makulli ya buga mata kai yayin da yake dukanta, kuma idan ta mutu to su sani mijin nata ne. wanda ya kashe ta.

The Punch

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *