Adebanjo ya ce Obafemi Awolowo ya yaki tsarin da turawan tsarin mulkin mallaka su ka zo da shi.
Alfijir Labarai ta rawaito an yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi kokari wajen ganin an ba shiyyoyi gashin kansu, a bar yankuna su iya tsayawa da kafafunsu.
Shugabannin Yarbawan kasar nan ta karkashin shugaban kungiyar Afenifere, Cif Ayo Adebanjo su kayi wannan kiran yayin taron.

An gudanar da taron shekara-shekara na GOAL a Lagos jagororin Yarbawa sun samu halarta.
A jawabinsa, Cif Ayo Adebanjo ya ce babu ta yadda za a cigaba sai an canza tsarin tafiyar da mulki, ya kuma yawa gwamnatin Bola Tinubu ta sauya salon mulki ta yadda shiyyoyi za su samu iko a doka
A cikin makon nan ne Daily Trust ta wallafa Ayo Adebanjo ya yi jawabi a wajen taron GOAL na wannan shekarar da aka gudanar a garin Legas.
An yi wa taron bana mai taken hadin kan yankin kudu maso yamma a karkashin inuwar VOR.
Jagoran na ‘yan Afenifire ya na cikin wadanda su ka gabatar da jawabi, har ya tuna da kokarin da Marigayi Obafemi Awolowo ya yi a lokacinsa.
Adebanjo ya ce Obafemi Awolowo ya yaki tsarin da turawan tsarin mulkin mallaka su ka zo da shi.
Dole Tinubu ya bi tafarkin Obafemi Awolowo.
Dattijon ya na ganin cewa idan ba a bar kowa ya ci gashin kan sa ba, za samu rashin cigaba a Najeriya, don haka ya yi kira da gwamnati mai-ci.
Adebanjo ya ankarar da Bola Ahmed Tinubu cewa duka shawarwarin da Awolowo ya kawo su na nan har yau, kuma za a iya aiwatar da su a kasar.
Obafemi Awolowo ya fadawa turawan mulkin mallaka cewa ba za su iya yin mulkin bai-daya a kasar nan ba.
Ya kamata sabon shugaban kasa ya canza tsarin mulkin tarayya ta yadda za a bar kowa ya tafi a yadda yake so.
Shugaban kungiyar DAWN da aka kafa domin cigaban Yarbawa, Mista Seye Oyeleye ya koka a game da rashin hadin-kai da yake damun kabilarsu.
Oyeleye ya bayyana cewa a yau mutanensa su na yi wa juna kallon jihohin da su ka fito, hakan ya kai ana jin haushi wajen rabon mukami.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb