Ganduje ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da shugaban kasa Bola Tinubu
Alfijir Labarai ta rawaito tsohon gwamnan jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana irin makiyayan da ke tada hankali a Najeriya.
Ganduje ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da shugaban kasa Bola Tinubu da hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Alhamis.
Tsohon shugaban na Kano ya bayyana cewa makiyayan da ke haddasa fitina su ne daga wajen kasar nan da kuma wadanda ke kaura daga Arewa zuwa Kudu.
A cewarsa, “Dukkan ku kun san cewa makiyaya iri hudu ne: wadanda suke zaune a gida kuma suna da dabbobinsu a kusa da gidajensu ba su haifar da wata matsala ba.
“Wani kuma makiyayan da ke fitowa daga sassan arewacin kasar nan zuwa tsakiyar Najeriya da kuma Kudancin Najeriya, suna haifar da matsaloli a kan hanyoyin; suran kuma wasu makiyaya ne da ke zuwa daga yammacin Afirka har zuwa arewacin Najeriya, har zuwa tsakiyar tsakiyar ƙasar , har zuwa kudanci, suna haifar da matsaloli da dama a kan tituna.
“Na hudu makiyaya ne da suka zauna a tsakanin wasu kabilu a Najeriya.
“Saboda a shekarun baya alakar da ke tsakanin makiyaya da manoma ce.
“Makiyaya suna samar da taki ga manoma, manoma kuma suna samar da wuraren kiwo ga makiyaya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb