Shugaban Najeriya ya amince a bawa waɗanda ambaliya ta shafa a Neja ₦2bn da tirelar shinkafa 20

FB IMG 1742320893164

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da fitar da naira biliyan biyu nan take domin sake gina dukkan gidajen da ambaliyar ruwa ta shafa a garin Mokwa na jihar Neja.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai garin Mokwa, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwar da ta lalata rayuka da dukiyoyi, tare da raba daruruwan mutane da muhallansu.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma ce Shugaban Ƙasar ya ba da izinin a gaggauta sakin manyan motoci 20 na shinkafa domin kai wa wadanda abin ya shafa.

Da yake tabbatar da cewa zuciyar Shugaba Tinubu na tare da jama’a, Shettima ya ce za a magance dukkan matsalolin da suka shafi jama’a.

A cewarsa, shugaban ya kuma bayar da umarnin a gyara gadojin da abin ya shafa a yankin ba tare da ɓata lokaci ba.

Dangane da batun magudanar ruwa kuwa, Shettima ya ce Shugaban Ƙasar ya kuma bayar da umarnin a gaggauta gyara magudanaN ruwa na garin Mokwa.

Gawarwaki fiye da 200
Sama da gawarwaki 200 ne aka samo bayan wata ambaliyar ruwa da ta yi ɓarna a al’ummomi a Mokwa a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025.

Kwamishinan agaji na jihar Neja, Ahmad Suleiman, ya ce har yanzu ana ci gaba da kokarin gano ƙarin wasu.

“An samu asarar rayuka fiye da 200 bisa la’akari da gawarwakin da aka gano zuwa yanzu, har yanzu muna ci gaba da zaƙulo gawarwaki.

“Babu wanda zai iya gaya muku adadin wadanda suka mutu a jihar Neja a halin yanzu domin har yanzu muna neman wasu gawarwaki,” in ji Suleiman yayin da yake magana a shirin ‘The Morning Brief’ gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.

Ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin kai daukin gaggawa domin rabon kayayyakin agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su, wadanda ke samun mafaka a sansanonin wucin gadi.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *