Alfijr ta rawaito Shugaban Kamfanin WhatsApp ya sanar da fitowar wani sabon salo wanda zai baiwa masu amfani da shi, damar gyara sakonnin da suka aika.
Tare da sabon fasalin, masu amfani da manhajar wajen aikewa da saƙon gaggawa za su iya gyara saƙonni ko da minti 15 bayan aika su.

Mark Zuckerberg, ne ya bayyana wannan ci gaba a yau Litinin.
Wannan dama zata yi amfani ne a lokacin da aka yi kuskure ko kuma son canza ra’ayi, yanzu haka damar gyaran saƙonnin ta samu.
“Muna farin cikin cewa yanzu za ku sami ƙarin iko akan maganganunku, kamar gyara rubutun da ba daidai ba ko ƙara bayani kan sakon da kuka aika.
Don yin wannan, a cikin minti 15 da aika saƙon, dole ne ku matsa kuma ku riƙe wannan saƙon na ɗan lokaci sannan ku zaɓi zaɓi na ‘Edit’ daga menu.”

Kafin wannan ci gaban, masu amfani da Whatsapp din kan goge sakonni ko rubuta wani gyaran a cikin wani sako na daban.
Sabon ci gaban ya riga ya fara fitowa ga masu amfani kuma zai kasance ga kowa a cikin ‘yan makonni masu zuwa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ