
Alfijr ta rawaito Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya amince da tsige sarakunan Piriga da Arak, Mai Martaba Jonathan Paragua Zamuna da Mai Martaba Janar Aliyu Iliyah Yammah (mai ritaya).
Kwamishiniyar kananan hukumomin jihar, Hajiya Umma Ahmad ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce, an sallami sarakunan biyu daga mukamin su a ranar Litinin 22 ga watan Mayun 2023.

Umma ta kara da cewa bayanan sun biyo bayan shawarwarin da ma’aikatar kananan hukumomi ta bayar ne bisa tanadin sashe na 11 na dokar kula da masarautun gargajiya mai lamba 21 ta shekarar 2021.
A cewar ta hakimin Garun Kurama, Babangida Sule, shi ne zai kula da al’amuran masarautar Piriga, har zuwa lokacin da za a nada sabon basaraken da zai maye gurbin wanda aka tsige, yayin da aka umurci sakataren majalisar da ya fara aikin nadin sabon Hakimin.

Sanarwar ta kara da cewa “gwamnati ta ga yadda martanin da Janar Iliyah Yammah ya bayar game da batun nadin hakimai hudu, sabanin wanda aka amince da su a masarautarsa ta Arak.
“Shi kuwa Korar Jonathan Zamuna ya biyo bayan rikicin kabilanci da ya barke tsakanin al’ummar Gure da Kitimi na Piriga a karamar hukumar Lere, da rashin zama a cikin masarautar.”
Hakazalika an sanar da sallamar hakiman kauyukan Aban, Abujan Mada da Anjil da ke masarautar Arak nan take.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Hakan yayi kyau kwarai Muna Godiya
Sa’annan Alfijr Kuma muna_yimuku fatan alkhairi, Allah Madaukaki yaqãra muku daukaka.
Ameen